Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Madagascar ta karbi gayyatar Afirka Ta Kudu ta wasan sada zumunta

Wasu 'yan wasan Bafana Bafana
Wasu 'yan wasan Bafana Bafana DR
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 min

Hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa babban tawagar kwallon kafar kasar, Bafana Bafana za ta ta fafata a wasan sada zumunta da Madasgascar a ranar 7 ga wannan wata na Satumba a filin wasa na Orlando da karfe 7 na yamma agogon GMT.

Talla

Wannan karawa dai ta maye gurbin wadda aka shirya yi tsakanin Bafana Bafana da Zambia a filin wasa na Independence Heroes na birnin Lusakan Zambia.

An soke wannan wasa ne sakamakon zakewar da hukumar kwallon kafar Zambia ta yi ne cewa bai kyautu a yi wani wasan sada zumunta ba a daidai lokacin da ake samun rikici mai nasaba da kin jinin baki ba.

Sakamakon haka, hukumar kwallon kafar Afirka Ta Kudu ta tuntubi Madagascar, wacce ta amince tawagar ta ta kara da Afirka Ta Kudun.

Kocin tawagar Bafana Bafana Molefi Ntseki ya bayyana jin dadinsa da wannan shiri na baya bayan nan, musammam ma ganin yadda ‘yan wasa daga kasashen waje suka hallaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.