Wasanni-Kwallon kafa

Ina ji zan dade a Roma - Smalling

Chris Smalling.
Chris Smalling. Reuters / Hannah McKay Livepic

Juma’ar nan tsohon dan wasan Manchester United kuma dan wasan Ingila da ya koma wasa aro a kungiyar kwallon kafa ta Roma a Italiya, Chris Smalling ya ce yana jin zai kasance a kungiyar ta Italiya na tsawon lokaci.

Talla

Ya ce wannan dama ce da ya ke bukata shi ya sa ma ya yi matukar daukin zuwa, kamar yadda yayi bayani yayin gabatar da shi a kungiyar.

Smalling, wadda ya buga wa Ingila wasa har sau 31 ya murza tamaula har 323 a zaman da yayi na shekaru 9 a Manchester United, inda suka lashe kofin Firimiyar Ingila har sau biyu.

Amma hasken sa ya dishe a kungiyar tun da United ta sayo dan wasan baya Harry Mcguire daga Leicester City kan kudi fam miliyan 80.

Roma ta biya kudi Yuro miliyan uku kafin ta sami dan wasan bayan na Ingila a matsayin aro.

Da ma Roma na da matsala a tsaron bayan ta tun da dan wasanta, dan kasar Girka Kostas Manolas ya koma Napoli kan kudi da aka ce ya kai yuro miliyan 36.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.