Wasanni

Salah zai iya kamo Messi da Ronaldo idan ya cire son kai- Wenger

Dan wasan gaba na Liverpool Mohammad Salah.
Dan wasan gaba na Liverpool Mohammad Salah. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce har yanzu Muhammad Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool na da cikakkiyar damar kamo takwarorinsa Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda a Juventus da kuma Lionel Messi na Argentina da ke taka leda a Barcelona, matukar ya cire son rai ya kuma ci gaba da zura kwallo kamar yadda ya faro a kakarsa ta farko da zuwa Liverpool.

Talla

Wenger a zantawarsa da wata jaridar wasanni, ya ce babu shakka kwazon dan wasan ya yi kasa bayan da ya fara nuna son kai wajen ganin lallai duk kwallon da ya dakko shi zai kai ta raga, wanda kuma a cewar tsohon kocin hakan na matsayin koma baya ga ‘yan wasa.

Wenger ya gwada misali da sabanin da ya faru tsakanin Salah da Mane a makon jiya, yayin wasan da suka lallasa Burnley da kwallaye 3 da 1 inda Salah ya ki bai wa Mane kwallo don ya zura a raga matakin da ya harzuka Mane.

Arsene Wenger wanda yanzu haka ya ke zaune ba tare da aikin yi ba, tun bayan ajje aikin horar da Arsenal bara bayan shafe shekaru 22 a waje guda, ya ce dole ne Salah ya kwaikwayi takwarorinsa Ronaldo da Messi wajen sanin lokacin da ya dace ya zura kwallo da kuma lokacin da ya kamata ya bayar da dama ga wasu su zura don ci gaba Club din, ko da dai ya ce shima Mane da Firmino dole sai sun sadaukar da wasu burukansu ta hanyar bayar da cikakkiyar dama ga Salah kamar dai yadda Suarez da Neymar suka yiwa Lionel Messi a Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI