Wasanni-Kwallon kafa

FIFA za ta ziyarci Iran game da kyale mata su yi kallon wasa

'Yan wasan tawagar kwallon kafar Iran
'Yan wasan tawagar kwallon kafar Iran ATTA KENARE / AFP

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta ce za ta aike da jami’anta Iran nan ba da jimawa ba, don nazari kan yiwuwar barin mata masu sha’awar kallon wasan kwallon kafa shiga filayen wasa.

Talla

Wannan sanarwar ta FIFA na zuwa ne mako daya bayan wata mai sha’awar kallon wasan kwallon kafa ta cinna wa kanta wuta kuma ta mutu murus, a wajen wani kotu bayan kotun ta shaida mata cewa tana iya zaman gidan yari na watanni shida saboda yunkurin ta na shiga irin ta maza don ta kutsa wani filin wasa a Tehran.

Hukumar mai kula da kwallon kafa ta duniya ba ta yi wani karin bayani game da ranar da za ta aike da ,jami’en na FIFA zuwa Iran, wacce aka dama da ita a gasar cin kofin duniya ta 2018 ba.

Wasu majiyoyi sun ce jami’en hukumar FIFA za su gana da hukumar kwallon kafar Iran amma, ba su tabbatar, ko musanta yiwuwar ganawa da mahukunta a Iran din ba.

Tun a shekarar 1981 Iran ta haramta wa mata shiga kallon wasan kwallon kafa, kuma malaman addini sun kare matakin suna cewa kokari ne na kare mata daga shiga inda maza suka fi rinjaye, da kuma kallon ‘yan wasan da kusan rabin jikinsu a waje ne.

Mutuwar Sahar Khodayari Ta janyo cece – ku ce a kafafen sadarwa na intanet, inda fitattun mutane da dama da ‘yan wasan kwallon kafa, suke ta kira ga FIFA da ta harmta wa Iran shiga duk wata sabga ta kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.