Wasanni-Kwallon kafa

Turan ya sha hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari

Arda Turan, dan wasan Barcelona
Arda Turan, dan wasan Barcelona Reuters

An yanke wa dan wasan tsakiya na Barcelona Arda Turan hukuncin daurin shekaru biyu da watanni 8 a gidan yari sakamkon samun sa da laifin harbi da bindiga da ya rikita, tare da razana wani, da kuma mallakar makami ba bisa ka’ida ba, da kuma ji wa wani rauni da gangan.

Talla

Shahararren dan wasan na Turkiyya da Barcelona, wadda ke wasa aro a kungiyar Istambul Basaksehir, ya samu sabani ne da wani mawaki dan kasar Turkiyya da ake kira Berkay Sahin, a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Rikicin ya yi wa Sahin sanadin karaya a hanci, kuma bayan haka ne Arda ya nufi asibitin da mawakin yake cikin dare, inda ya zare bindiga ya yi harbin iska inda ya tsorata mutane.

An tuhumi Arda da laifin cin zarafin matar mawakin, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, ji wa wani rauni da gangan, da kuma harbi da bindiga.

Tuni dai kungiyar 
Basaksehir ta tabbatar da cin tarar dan shekaru 32 din lira miliyan 2 da rabi na kudin Turkiyya, daidai da Yuro sama da dubu 350.

Sai dai game da batun hukuncin, Arda ba zai shiga gidan yari ba, hukuma za ta sa mai ido ne na shekaru 5, wadda idan ya aikata laifi a tsakani za ta garkame shi.

Bayan ya bayyana a kotu a ranar Laraba, Arda ya wallafa sakon twitter da ke cewa bai aikata laifin ba, kuskure ne ya yi,kuma ake amfani da shi wajen yi masa batanci.

A shekarar 2015 dan wasan ya koma Barcelona kan kudi Yuro miliyan 35,inda ya buka mata wasanni 55 a dukkannin gasanni kafin a bayar da shi aro ga kungiyar Basaksehir.

Wasanni 100 ya buga wa tawagar kwallon kafar Turkiyya, inda ya ci mata kwallaye 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.