Wasanni-Kwallon kafa

Barcelona da Real Madrid na rige-rigen sayen Van Dijk na Liverpool

Virgil van Dijk, bayan nasararsa ta lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara na Turai
Virgil van Dijk, bayan nasararsa ta lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara na Turai REUTERS/Eric Gaillard

Wasu rahotanni a Spain na cewa kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da Real Madrid na rige-rigen saye dan wasan baya na Liverpool Virgil van Dijk baya ga kulla kwantiragi da mai horar da kungiyar Jurgen Klopp.

Talla

Jaridar wasanni ta Daily Star ta ruwaito cewa tun a kakar musayar ‘yan wasan da ta gabata cikin watan Agusta kungiyoyin biyu suka tuntubi Liverpool game da dan wasan yayinda suka tattauna kai tsaye da Klopp wanda ke cikin jerin masu horarwa 3 da za a fitar da zakara ciki.

Haka zalika shima Van Dijk na cikin jerin ‘yan wasa 3 da za a fitarda zakaran da zai lashe kyautar Ballon d’Or a cikinsu, kuma matukar ya yi nasara, zai zamo karon farko da wani dan wasa ya lashe kyautar ba daga kungiyar kwallon kafa daga Spain ba, tun bayan Cristiano Ronaldo da ya lashe a shekarar 2008 lokacin ya na Manchester United.

Jaridar dai ta bayyana cewa tun a wancan lokaci, Liverpool ba ta amince da bukatar ta Barcelona da kuma Real Madrid ba, matakin da ya sanya Real Madrid tuntubar van Dijk ta bayan fage ko da dai babu alamun samun nasara.

Kungiyoyin biyu dai na Barcelona da Real Madrid ana ganin suna son amfani da Klopp ne don maye gurbin manajojinsu da suka kora, bayan da Klopp ya samu nasarar kai Liverpool ga nasarar dage kofin zakarun Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.