Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Rayuwar shahara ba dadi - Ronaldo

Cristiano Ronaldo dan wasan Juventus da Portugal
Cristiano Ronaldo dan wasan Juventus da Portugal Ảnh REUTERS

Shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, mai wasa a Juventus ta Italiya ya bayyana yadda shahara ke ci masa tuwo kwarya, inda yake cewa, ba ya iya kai ‘yayan sa wajen wasa ko shakatawa saboda fargabar kada a shaida shi a hana shi sakat.

Talla

Cristiano Ronaldo ya ce shahara ta sa yanzu rayuwarsa babu armashi, kuma yana so ya samu sa’ida.

Dan shekarar 34 din yana daga cikin mutane mafi shahara a duniya, inda ya shafe akasarin shekarun da ya yi yana murza tamaula a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi iya murza ta a duniya.

Baya ga lashe lambobin yabo da kofuna da Manchester United, Real Madrid da Juventus, dan wasan gaban ya jagoranci tawagar kwallon kafar Portugal zuwa lashe kofin nahiyar Turai, sannan ya ci kyautar shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya, Ballons d’Or har sau biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.