Wasanni-Kwallon kafa

Ina bukatar karin Ballon d'Or 2 ko 3 kafin na yi ritaya- Ronaldo

Cristiano Ronaldo bayan lashe kyautar Ballon d'Or karo na 5
Cristiano Ronaldo bayan lashe kyautar Ballon d'Or karo na 5 AFP/L'Equipe/Franck Faugère

Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo ya ce yana fatan sake lashe kyautar Ballon d’Or akalla sau biyu ko uku kafin ritayarsa daga fagen tamaula.

Talla

Ronaldon wanda ya lashe kyautar ta Ballon d’Or har sau 5 dai dai da Lionel Messi na Argentina da ke taka leda a Barcelona, a wata tattaunawarsa da ITV ya ce yana fatan dara takwaran nasa yawan kyautukan Ballon d’Or.

Ronaldo dan Portugal mai shekaru 34 ya ce duk da kasancewarsa a jerin ‘yan wasan kwallon kafa da suka kafa gagrumin tarihi a fagen, yana fatan sake kafa wani tarihin kafin barinsa fagen.

Bayan nasarar Luka Modric ta lashe ballon d’Or a bara, shekaru 10 da suka gabata ‘yan wasan biyu su ke lashe kyautar, yayinda ko a bana ma dai sunayen Cristiano Ronaldon da Lionnel Messi na cikin wadanda ake saran su iya lashe kyautar ta Ballon d’Or tare da Virgil van Dijk na Liverpol dan kasar Holland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.