Isa ga babban shafi
Wasanni

Akwai jan aiki a gaban Manchester United

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya bukaci 'yan wasansa su kara kaimi wajen zura kwallaye a ragar abokan hamayya
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya bukaci 'yan wasansa su kara kaimi wajen zura kwallaye a ragar abokan hamayya REUTERS / Marcelo del Pozo
Minti 2

A karon farko cikin shekaru 30, Manchester United ta fara kakar wasanni mafi muni bayan ta samu maki tara daga cikin wasanni bakwai da ta buga a gasar firimiyar Ingila, inda Liverpool mai jan ragamar teburin ta ba ta tazarar maki 12.

Talla

Kungiyar ta yi fatan samun nasara a karan-battan da ta yi da Arsenal  a Old Trafford, amma suka tashi kunnen doki 1-1.

Pierre Emerick Aubameyang na Arsenal ne ya haramta wa Manchester United samun nasara a karawar, inda ya jefa mata kwallo a raga a minti na 58, abin da ya soke kwallon da Manchester ta fara zurawa a minti na 45 ta hannun Scott Mc Tominay.

Da farko, an soke kwallon da Aubameyang ya zura saboda zaton cewa, ya yi satar fage, amma daga bisani, na’urar taimaka wa alkalin wasa, ta tabbatar da ingancin kwallon.

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce, akwai bukatar ‘yan wasansa su kara kaimi wajen samun nasara a wasanninsu, musamman ganin yadda ba sa iya zura kwallo fiye da guda a ragar abokan hamayyarsu a sabuwar kakar.

Kungiyoyin Manchester United da Arsenal sun taba kasancewa manyan zakarun Ingila tsakanin shekarar 1996 zuwa 2004, inda a wancan lokacin babu kamarsu a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.