Isa ga babban shafi
Wasanni

Ana cacar kudi kan sallamar kocin Manchester United

Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer
Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer Reuters/Lee Smith
Minti 1

Magoya bayan Manchester United sun fara sanya kudi a wata caca, inda suke da kwarin guiwar cewa, nan kusa kungiyar za ta sallami kocinta Ole Gunnar Solskjaer daga bakin aikinsa.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ta sha kashi a hanun Newcastle da ci 1-0 a karawar da suka yi a ranar Lahadi a gasar firimiyar Ingila.

Wasu daga cikin ‘yan cacar na ganin cewa, akwai yiwuwar kocin Everton Marco Silva ko kuma kocin Tottenham Mauricio Pochettino, daya daga cikinsu ne zai zama sabon kocin Mancheter United.

Sai dai hankalinsu ya fi karkata kan Pochettino na Tottenham wanda shi ma ke cikin tsaka mai wuya a kungiyarsa.

Shekaru 30 kenan raban da Manchester United ta gamu da farkon kaka mara armashi a gare ta, inda a yanzu take matasyi na 12 akan teburin gasar ta firimiya, wato maki 2 tsakaninta da matakin ‘yan dagaji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.