Wasanni

Dalilan da suka hana wasan dambe ci gaba a Najeriya

Sauti 09:59
Wasan dambe na da muhimmaci a kasashen Hausa
Wasan dambe na da muhimmaci a kasashen Hausa RFI HAUSA

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya kai ziyara ne jihar Bauchin Najeriya, inda ake gudanar da wata gasar damben gargajiya. Wasan dambe na da muhimmanci a kasashen Hausa, amma har yanzu yana fuskantar koma-baya a Najeriya a daidai lokacin da kasashen Afrika irinsu Nijar da Senegal ke ci gaba da bunkasa harkar. A cikin wannan shirin za ku ji abin da masana ke cewa kan dalilan da suka hana wasan dambe samun ci gaban azo a gani a Najeriya.