Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

FIFA ta dakatar tsohon shugaban hukumar kwallon kafar El-Salvador har abada

Shugaban FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino. REUTERS/Naseem Zeitoon/File Photo
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 min

Hukumar kwallon kafar Duniya FIFA, a yau Litinin ta ce ta haramta wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar El- Savador, Reynaldo Vasquez shiga duk wata sabga ta kwallon kafa har abada.

Talla

A shekarar 2017 wata Kotu a El- Salvador dai ta yanke wa Vasques hukuncin daurin shekaru 8 a gidan yari biyo bayan zarginsa da kwanciyar magirbi a wasu damasheren kudade.

A yau Litinin FIFA ta haramta mai shiga harkar wasanni har iya tsawon rayuwarsa, sannan ta ci shi tarar sama da dalar Amurka dubu dari 5, sakamakon rashawa da aka sameshi da hannu dumu – dumu a ciki, har da lamushe kudaden wasannin sada zumunta tsakanin shekarun 2009 – 2015.

Shine tsohon jami’in FIFA, dan nahiyar yammacin Amurka na baya – bayan nan da aka yi wa irin wannan haramci na shiga sabgar kwallon kafa na har abada – abadin.

Wannan haramcin da aka mai ya biyo bayan na tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Uruguay Eugenio Figueredo da Juan Angel Napout, tsohon shugaban hukumar kwallon Paraguay, da na Colombia Enrique Sanz.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.