Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Platini zai dawo harkar kwallon kafa bayan dakatarwa

Michel Platini, a shelkwatar FIFA  dake Zurich a Switzerland
Michel Platini, a shelkwatar FIFA dake Zurich a Switzerland REUTERS/Arnd Wiegmann
Zubin rubutu: Michael Kuduson
1 min

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Michel Platini, ya kammala wa’adin dakatarwa da aka kakaba mai a harkar kwallon kafa, bayan karya dokar da yayi, kuma yana iya dawowa harkar, sai dai da sauran rina a kaba, saboda har yanzu akwai binciken da ake mai a kasar sa Faransa, a kan zargin hannu a rashawa da ke da nasaba da gasar kofin Duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022.

Talla

Tsohon kaftin, kuma tsohon kocin tawagar kwallon kafar Faransa, wanda sau 3 yake lashe kyautar Balon d’Or, ya zama jagoran harkar kwallon kafa mafi fice, bayan an zabe shi a matsayin shugaban hukumar kwallon kafar Turai a shekarar 2002.

An dakatar da shi daga shiga harkar kwallon kafa bayan an same shi da laifin karbar na goro da ya kai dalar Amurka miliyan 2 da shi da shugaban hukumar kwallon kafar Duniya Sepp Blatter.

Platini, mai shekaru 64, wadda ke kokarin wanke kansa da sunansa yana iya shiga harkar kwallon kafa a ranar Litinin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.