Wasanni

Real Madrid na son sayen Kante daga Chelsea

Ngolo Kanté
Ngolo Kanté FRANCK FIFE / AFP

Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta shirya tsaf domin takara da Juventus wajen kokarin sayo dan wasan Chelsea, N'golo Kante kamar yadda jaridar Mail ta rawaito.

Talla

Dan wasan na Faransa ya nuna kansa sosai musamman a lokacin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, sannan kuma ya na daya daga cikin zaratan ‘yan wasan tsakiya da a yanzu ake ji da su, abin da ya sa Real Madrid ta fara tunanin dauko shi.

Madrid na tantama kan Casemiro, tana ganin ba shi da karsashin ci gaba da rike mata tsakiya, shi ya sa ta fara hararo Kante.

Real Madrid a shirye take ta bayar da zunzurutun farashin Pam milyan 70 domin sayo dan wasan mai shekaru 28.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.