Wasanni

Solksjaer ya zargi 'yan wasansa da shirya masa tuggu

Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer.
Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer. REUTERS/Andrew Yates

Mai horas da Manchester United Ole Gunnar Solkjaer ya yi tur da rashin kwazon 'yan wasansa, tare da zarginsu da kokarin haddasa korar shi daga bakin aiki.

Talla

Dangantaka na neman yin tsami tsakanin Solkjear da yan wasansa ne tun, bayan kayen da suka sha a hannun Newcastle yayin fafatwarsu a gasar Premier a karshen mako.

Rashin nasarar ta United a ranar lahadi, ta sanya ta koma matsyi na 12 a jerin kungiyoyi 20 dake fafatawa a gasar Premier ta bana.

A halin yanzu kocin Manchester United na fuskantar matsin lamba kan gaggauta gyara matsalolin da suke fuskanta, duk da cewar a watan jiya, mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodward ya ce zai ci gaba da mara mishi baya.

Rahotannin da muka samu a baya bayan nan ma sun ce mai yiwuwa Manchester United din ta sallami Solkjaer cikin wannan wata, muddin kungiyar ta sha kaye a wasan da za ta fafata da Norwich City a ranar 20 ga Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.