Wasanni

Ramos ya kafa tarihin bugawa Spain adadin wasanni mafi yawa

Sergio Ramos da Andres Iniesta.
Sergio Ramos da Andres Iniesta. FELIX ORDONEZ REUTERS

Sergio Ramos ya kafa tarihin zama dan wasan da ya zarta takwarorinsa na Spain bugawa tawagar kwallon kafar kasar wasanni.

Talla

Kaftin din na Real Madrid ya kafa tarihin ne, bayan wasan neman cancantar halartar gasar kwallon kafa ta cin kofin kasashen Turai, da suka tashi 1-1 da kasar Norway a ranar asabar.

A halin yanzu Ramos ya bugawa Spain wasanni 168.

Cikin watan Maris na 2005, Ramos ya soma wakiltar Spain a ajin manya yayin fafatawa da kasar China.

Sauran ‘yan wasan Spain da ke biye da Sergio Ramos wajen adadin wasannin da suka bugawa Spain sun hada da, mai tsaron raga Iker Casillas da ya buga wasanni 167, sai Xavi mai wasani 133, da kuma Andres Iniesta da ya wakilci Spain a wasanni 131.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.