Laliga na son a sauya wajen da wasan Classico zai gudana

'Yan wasan Barcelona da Real Madrid
'Yan wasan Barcelona da Real Madrid REUTERS/Juan Medina

Hukumar da ke shirya gasar Laliga ta bukaci hukumar kwallon kafar Spain ta sauya tsarin wasan El Classico da zai gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar 26 ga watan nan, sakamakon zanga-zangar da ke ci gaba da tsananta a yankin Catalonia.

Talla

Hukumar kwallon kafar Spain dai ta tsara cewa wasan manyan kungiyoyin biyu karkashin gasar Laliga zai gudana ne a filin wasan Barcelona na Camp Nou kenan wanda ya ke a yankin Cataloniar, sai dai Laliga ta bayyana shakku game da yiwuwar wasan inda ta nemi a mayar da shir Madrid babban birnin kasar.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa ‘yan awaren Catalonia sun shirya wani gagarumin gangami a ranar da aka tsara karawar tsakanin Real Madrid da Barcelonar wasan da ake yiwa Lakabi da El Classico karkashin gasar Laliga wadda yanzu Real Madrid ke jagorancin teburinta da maki 18 tazarar maki 2 tsakaninta da Barcelonar a matsayin ta biyu bayan doka wasanni 8 kowannensu.

Yanzu haka dai hukumar kwallon kafar ta Spain wadda ta karbi korafin na Laliga ta ce tana dakon ra’ayinkungiyoyin biyu zuwa nan da litinin din makon gobe kafin yanke hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI