Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya lashe takalmin zinaren gasar zakarun Turai na 6

Lionel Messi, bayan lashe kyautar takalmin zinare na 6.
Lionel Messi, bayan lashe kyautar takalmin zinare na 6. Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Gwarzon dan kwallon kafa na duniya, zalika kaftin din Barcelona Lionel Messi, ya karbi kyautar takalmin Zinare karo na 6, bayan zura adadin kwallaye mafi yawa tsakanin takwarorinsa dake manyan gasannin nahiyar Turai.

Talla

Messi ya lashe takalmin Zinaren ne, da adadin kwallaye 36, yayinda wanda suka yi takarar neman kyautar Kylian Mbappe na PSG yake da kwallaye 33.

Karo na 3 kenan da Messi ke lashe kyautar takalmin Zinaren a jere, bayan da ya lashe kyautar a shekarun 2010, 2012 da kuma 2013, abinda ya bashi damar zarta abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo da takalman Zinaren 2, wanda ya taba lashe kyautar sau 4.

Tun daga shekarar 2009 da dan wasan Atletico Madrid Diego Forlan ya lashe kyautar zuwa bana, 'yan wasan dake kungiyoyin Spain ne ke lashe kyautar takalmin zinaren na Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.