Isa ga babban shafi
Wasanni

Tottenham ta soma tuntubar tsohon kocin United

José Mourinho, tsohon kocin kungiyoyin Manchester United, Chelsea da Real Madrid.
José Mourinho, tsohon kocin kungiyoyin Manchester United, Chelsea da Real Madrid. AFP/Thomas Coex
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Kungiyar Tottenham ta soma tuntubar Jose Mourinho, tsohon kocin Manchester United da Real Madrid kan yiwuwar karbar ragamar horas da 'yan wasanta.

Talla

Tottenham ta soma yunkurin ne, biyo bayan rashin tabuka abin azo a gani da ‘yan wasanta ke yi bayan soma kakar wasa ta bana, a karkashin kocin kungiyar na yanzu Mauricio Pochettino, inda a baya bayan nan suka sha kaye a hannun Bayern Munich da 7-2 a gasar zakarun Turai.

Tun bayan sallamarsa da Manchester United tayi, Maourinho bai sake kulla yarjejeniya da wata kungiya ba, wanda kuma ya sha yin watsi da tayin wasu kungiyoyin, ciki har da Benfica da kuma Lyon a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.