Wasanni

Zidane ya janye bukatar sayen Pogba

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinadine Zidane ya janye kudirinsa na ganin Club din ya yi cinikin Paul Pogba daga Manchester United bayan gaza cimma matsaya tsawon lokaci.

Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba
Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba REUTERS
Talla

Pogba dan Faransa, wanda tun a waccan kaka, ake tattaunawa game da yiwuwar komawarsa Real Madrid amma kuma aka gaza cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu, inda tsohon dan wasan na Juventus ya ci gaba da zama a Manchester United tare da fuskanta tarin taunuka a wannan kaka.

Wasu bayanai sun nuna cewa yanzu haka Zidane a janye daga bukatar ta sayen Pogba yayinda zai maye gurbinsa da wani dan wasa daban yayin kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa wargajewar cinikin ya biyo bayan farashin yuro miliyan 180 da United ta sanya kan Pogba wanda shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ce bai shirya biyan dan wasan farashin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI