Isa ga babban shafi
Wasanni

Man City za ta karawa Sterling albashi don hana shi zuwa Madrid

Dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Raheem Sterling.
Dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Raheem Sterling. REUTERS/David Klein
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City na shirin mikawa Raheem Sterling tayin biyansa yuro dubu 450 kowanne mako don dakile yunkurin Real Madrid na saye shi a kakar musayar ‘yan wasan da ke tafe.

Talla

Sterling dan Ingila wanda a watan Nuwamban bara ya sanya hannu kan kwantiragin da zai kai shi shekarar 2023 inda Cityn ke biyanshi yuro miliyan 280 kowanne mako, amma ya jima ya na bayyana ra’ayinsa na fatan taka leda a wajen Ingila.

Jaridar wasanni ta Sunday Express ta ruwaito cewa Mai horar da kungiyar ta Manchester City Pep Guardiola na son Club din ya mayar da Sterling mai shekaru 24 mafi daukar kudi tsakanin takwarorinsa na Ingila na hana shi barin club din.

Toshon dan wasan na Liverpool yanzu haka ya shiga sahun zakakuran ‘yan wasa na duniya bayan rawar da ya taka a kakar wasan da ta gabata dama kokarinsa a wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.