Wasanni

'Yan jagaliya sun jikkata magoya bayan Bayern Munich

Wasu daga cikin magoya bayan Bayern Munich a filin wasa na Olympiakos a Girka
Wasu daga cikin magoya bayan Bayern Munich a filin wasa na Olympiakos a Girka Reuters

Bayern Munich ta shigar da kara a gaban Hukumar Kwallon Kafa ta Turai bayan an soke wasanta a gasar Lig ta matasa da Olympiaos sakamakon tashin hankalin da ya kai ga jikkata magoya bayanta.

Talla

Bayern Munich ta ce, an kwantar da magoya bayanta da dama a asibiti bayan wasu ‘yan jagaliya rufe da fuskokinsu sun kai musu hari a yayin wasan.

Bayern Munich wadda ita ca zakarar Jamus, na samun nasara da kwallaye 4-0 a yayin karawar kafin daga bisani a soke wasan a minti na 84.

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai ta tabbatar cewa, tana kan gudanar da bincike game da lamarin kafin daukar mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.