Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Super Eagles rike kanbunta 3 a Afrika cikin jadawalin FIFA

Mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles Gernot Rohr tare da wasu 'yan wasa.
Mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles Gernot Rohr tare da wasu 'yan wasa. Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta yi kasa da maki daya a jadawalin hukumar FIFA kan kasashe mafi iya kwallo na duniya inda yanzu take a matsayin ta 35.

Talla

A rahoton na FIFA yanzu haka Najeriyar na da maki 1481 ne kasa da 1482 da ta samu a watan Satumba, duk kuwa da yadda kasar ta yi nasarar canjaras tsakaninta da Brazil yayin wasan sada zumuntan da ya gudana tsakaninsu.

Sai dai duk da rashin makin guda cikin wannan watan har yanzu Super Eagles ita ke matsayin ta 3 a nahiyar Afrika kasa da Senegal a matsayin ta 1 da kuma Tunisia a matsayin ta 2 amma kuma sama da Algeria mai rike da kambun Afrika.

A matakin duniya, kasashen na Senegal da Tunisia sun yiwa Najeriyar fintinkau inda su ke a matsayin na 20 da kuma 29 da maki 1546 da kuma 1495.

Duk dai karkashin jadawalin na FIFA Belgium ta ci gaba da kasancewa lamba 1 a fagen na Tamaula haka zalika France ta rike matsayin na lamba 2 yayinda itama Brazil ke matsayinta na lamba 3.

A bangaren ‘yan goman farko na jadawalin an dan samu sauyi a wannan karon Inda Uruguay ta dawo ta 5 Croatia ta 7 Argentina kuma ta 9 dukkanninsu sun daga da maki daddai.

Kasashen da ake ganin sun matukar nuna hazaka a wannan watan akwai Ukraine wadda ta matsa da matakai 3 inda yanzu take matsayin ta 22 haka zalika Japan da mataki 3 inda yanzu ta ke matsayin ta 28 sai Turkiya wadda ta matsa da mataki 4 a matsayin ta 32 kana Rasha wadda ta matsa da mataki 5 a matsayin ta 37.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.