Wasanni

Pulisic ya kafa sabon tarihi a Chelsea

Dan wasan gaba na Chelsea Christian Pulisic.
Dan wasan gaba na Chelsea Christian Pulisic. Reuters/Lee Smith

Christian Pulisic ya kafa tarihin zama dan wasan Chelsea mafi karancin shekaru da ya ci wa kungiyar kwallaye uku a wasa guda "wato hat-trick" a turance.

Talla

Pulisic ya kafa tarihin ne yayin wasan gasar Premier da suka lallasa Burnley da kwallaye 4-2 a asabar din da ta gabata.

A watan Satumban da ya gabata dan wasan Chelsea Tammy Abraham ya soma kafa tarihin na zama mafi karancin shekarun da ya ci wa kungiyar kwallaye uku a wasa guda, yayin fafatawar da suka lallasa Wolves da kwallaye 5-2. A lokacin Abraham ya yi bajintar ce yana da shekaru 21 dakwanaki 347.

Sai dai a asabar din da ta gabata, Pulisic ya goge tarihin bayan cin kwallaye ukun a wasa guda yana da shekaru 21 da kwanaki 38.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.