Wasanni-Kwallon kafa

Sai a Disamba Pogba zai dawo wasa - Solskjaer

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. Reuters

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce mai yiwuwu has dan wasan tsakiya na kungiyar, Paul Pogba ba zai dawo fagen tamaula ba har sai watan Disamba.

Talla

Dan wasan mai shekarau 26 ya samu rauni a idon sawunsa ne tun a ranar 30 ga watan Satumba, kuma wasanni 6 ne kawai ya buga wa kungiyarsa tun da aka fara wannan kakar wasanni, biyo bayan alakanta shi da komawa Real Madrid.

Bayan ya dan yi hutu a Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, don ya samu lokacin murmurewa, kocinsa ya ce har yanzu zai yi zaman wata daya ba tare da ya murza leda ba.

Manchester United a jiya Lahadi ta taka rawar ganin a wasan ta da Norwich ba tare da Pogba ba, inda ta yi nasara 3-1, lamarin da ya sa ta kawo karshen wasanni 4 a jere ba tare da nasara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.