Wasanni

Manyan kungiyoyin Turai na takara kan dan wasan Najeriya

Manyan Kungiyoyin nahiyar Turai na ci gaba da shiga sahun wadanda ke son kulla yarjejeniya da dan wasan tawagar kwallon Najeriya ta Super Eagles Victor Osimhen dake taka leda a kungiyar Lille a gasar Ligue 1 ta Faransa.

Dan wasan Najeriya a tawagar Super Eagles, Victor Osimhen dake kungiyar Lille a kasar Faransa.
Dan wasan Najeriya a tawagar Super Eagles, Victor Osimhen dake kungiyar Lille a kasar Faransa. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Osimhen mai shekaru 20, yanzu haka shi ne dan wasa na uku mafi daraja a gasar kwallon kafarta Faransa a jin matasa.

Hakan tasa a baya bayan nan kungiyoyin Bayern Munich da AC Milan suka soma kokarin jan ra’ayin dan wasan domin kulla yarjejeniya da shi.

A makwannin bayan dai, rahotanni sun ce Barcelona, Manchester United da kuma Newcastle sun bayyana aniyar kulla yarjejeniya da Victor Osimhen, wanda a kakar wasa ta bana, ya ci wa kungiyarsa ta Lille kwallaye 8 a wasanni 14 da ya buga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI