Wasanni-Kwallon kafa

Muna iya kaurace wa wasan Carabao -Klopp

Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila.
Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila. REUTERS/Charles Platiau

Mai horar da ‘yan wasan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce kungiyar na iya kaurace wa wasan daf – da – na – kusa – da karshe a gasar kofin Carabao har sai an sanya wasan a lokacin da ya dace.

Talla

Liverpool ta samu zuwa wannan mataki na quarter finals ne bayan sau biyu ta taso daga baya ta farke kwallayen da Arsenal ta saka a ragarta lamarin da ya sa wasa ya kare canjaras 5-5 bayan mintuna 90, sannan ta doke Arsenal din a bugun fenariti.

Hukumar kula da gasar League ta kasar Ingila dai na shirin sanya wasannin daf – da – na - kusa – da – karshe a ranar 16 ga watan Disamba, kuma a ranar 18 ga watan Disamba ce Liverpool za ta fafata a wasan kusa da karshe na gasar kofin kungiyoyin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI