Wasanni

Bayern Munich ta sallami kocinta

Niko Kovac da Bayern Munich ta sallama daga aikin koci
Niko Kovac da Bayern Munich ta sallama daga aikin koci Reuters

Kungiyar Kwallon Kafa ta Bayern Munich ta sallami kocinta Niko Kovac bayan lallarsa da ta sha a hannun Eintracht Frankfurt da ci 5-1 a ranar Asabar da ta gabata a gasar Bundesliga.

Talla

Kocin ya lashe wasanni 45 daga cikin wasanni 65 da ya jagoranci kungiyar, amma lallasar da suka sha a ranar Asabar, ita ce mafi muni a gare ta a cikin shekaru 10 a tarihin gasar Bundesliga.

Yanzu haka kungiyar na matsayi na hudu a teburin gasar, inda Borussia Monchengladbach da ke jan jan ragama ta ba ta tazarar maki hudu.

Tuni mataimakin koci, Hansi Flick ya shirya tsaf domin maye gurbin Kovac, kuma shi ne zai jagoranci kungiyar a wasan da za ta yi da Olympiakos a ranar Laraba a gasar Zakarun Turai da kuma wasan da za su yi da Borussia Dortmund a ranar Asabar mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI