Wasanni

Hankalin 'yan wasan Ingila ya tashi saboda Gomes

Lokacin da Gomes ke kwance a kasa bayan samun mummunan rauni a wasan Everton da Tottenham a gasar firimiyar Ingila a karshen mako
Lokacin da Gomes ke kwance a kasa bayan samun mummunan rauni a wasan Everton da Tottenham a gasar firimiyar Ingila a karshen mako Reuters

Andre Gomes na Everton ya gamu da mummunan rauni a kafarsa, lamarin da ya sa dan wasan Tottenham, wato Son Heung-min zubar da hawaye, yayin da sauran takwarorinsa suka shiga alhini saboda tashin hankalin da suka gani na raunin dan wasan.

Talla

Son ne ya kai wa Gomes hari ta baya, abin da ya sa ya yi muguwar faduwa, inda 'yan wasan da ke kan fili da wasu daga cikin 'yan kallo na kusa-kusa suka mayar da zazzafan martani nan take.

Wasu daga cikin ‘yan wasan sun dora hannayensu a ka, tare da nuna yanayi na alhini, lura da girman raunin da dan wasan ya samu.

An garzaya da Gomes dan asalin kasar Portugal zuwa asibiti, inda aka tabbatar cewa, ya samu zagewa da kuma gocewar kashi lokaci guda a kafarsa, yayin da ake sa ran yi masa tiyata a wannan Litinin.

Sai da aka dakatar da ci gaba da wasan na firimiyar Ingila tsakanin kungiyoyin biyu na tsawon minti 6, saboda likitocin da suka fantsama kan fili domin duba lafiyar Gomes.

Tuni aka bai wa Son jan kati a wasan wanda suka tashi kunnen doki 1-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI