Wasanni-Kwallon kafa

Ba zan yi biris da Bayern Munich ba - Wenger

Tsohon mai horar da 'yan wasan Arsenal, Arsenal Wenger.
Tsohon mai horar da 'yan wasan Arsenal, Arsenal Wenger. Reuters/Scott Heppell

Tsohon mai horar da’yan wasa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya yi bayanin yadda yake sha’awar kugiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, abin da ke dada sa wa ake tunanin zai yi aiki da kungiyar.

Talla

Arsene Wenger bai ce ba zai horar da kungiyar ba idan ya samu dama, biyo bayan rahotannin da ke cewa yana hanyarsa ta zuwa kungiyar tun da ta sallami Niko Kovac.

Dan shekara 70 din bai samu aikin horar da wata kungiya ba tun da ya yi hannun riga da Arsenal a kakar wasanni ta 2018, amma ya sha zakewa cewa yana da sha’awar komawa aikin horar da’yan wasan tamaula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI