Wasanni

Anya Manchester City za ta kamo Liverpool kuwa?

Lokacin da Mohamed Salah ya ci kwallo ta biyu a fafatawarsu da Manchester City a Anfield
Lokacin da Mohamed Salah ya ci kwallo ta biyu a fafatawarsu da Manchester City a Anfield Carl Recine/Reuters

Liverpool ta kama hanyar lashe kofin gasar firimiyar Ingila karo na farko cikin shekaru 30 bayan ta lallasa mai rike da gambin gasar wato Manchester City da kwallaye 3-1 a Anfield. Pep Guardiola ya ce, bai sani ba ko za su iya kulle tazarar da Liverpool ta ba su a teburi.

Talla

Yanzu haka Liverpool na jan ragamar teburin da maki 34, inda ta bai wa Manchester City tazarar maki 9.

Liverpool ta jefa kwallaye biyu cikin ragar City a cikin mintina 13 na farko ta hannun Fabinho da Mohamed Salah, kafin Sadio Mane ya kara ta uku bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A karo na uku kenan da Manchester City ke shan kashi a wasanni takwas na gasar firimiyar Ingila a bana, abin da ke nuna cewa, akwai gagarmin aiki a gabanta muddin tana son kare wannan kambi da ke hannunta.

Kodayake ya yi wuri a tsayar da hasashe kan kungiyar da za ta lashe gasar ta bana, lura da cewa, akwai sauran wasanni da dama da za a yi nan gaba.

Watakila saboda haka ne, kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya bayyana cewa, akwai sauran aiki a gabansu duk da cewa, sun bai wa Manchester City tazarar maki 9.

A cewar kocin, jan ragamar teburin gasar a cikin watan Mayun badi, ita ce mafi muhimmanci amma ba a cikin wannan wata na Nuwamba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI