Wasanni

Bana sha'awar kulla yarjejeniya da Arsenal - Enrique

Tsohon mai horas da Barcelona Luis Enrique.
Tsohon mai horas da Barcelona Luis Enrique. REUTERS

Tsohon mai horas da Barcelona, da kuma tawagar kwallon kafar Spain, Luis Enrique, yace ko kadan baya sha’awar kulla yarjejeniyar zama sabon kocin Arsenal.

Talla

Enrique ya bayyana haka ne a dai dai lokacin da wasu rahotanni ke cewa Arsenal din na shirin tuntubarsa a hukumance, wasu kuma ke cewar kungiyar ta ma soma tattaunawa da shi don maye gurbin kocin ta na yanzu Unai Emery.

Emery ya soma fuskantar suka ne bayan wasan da Leicester City ta lallasa Arsenal da kwallaye 2-0, abinda yasa yanzu haka kungiyar ta koma matsayi na 6 a gasar Premier, maki 8 tsakaninta da Manchester City dake matsayi na 4.

Sai dai a jiya litinin hukumar gudanarwar kungiyar ta Arsenal ta bayyana goyon bayanta ga Unai Emery, amma tare da gargadin ya zama dole, kungiyar ta koma samun nasarori sabanin abinda take fuskanta a yanzu.

A baya bayan nan dai wasanni 2 daga cikin 10 kawai Arsenal ta samu nasarar lashewa a gasar Premier.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.