Wasanni

Mai yiwuwa Ronaldo ya fuskanci haramcin wasannin shekaru 2

Cristiano Ronaldo cikin fushi, yayin ficewa daga filin wasan fafatawa da AC milan, bayan maye gurbinsa da Paulo Dybala.
Cristiano Ronaldo cikin fushi, yayin ficewa daga filin wasan fafatawa da AC milan, bayan maye gurbinsa da Paulo Dybala. Reuters

Mai yiwuwa Ronaldo ya fuskanci tsattsauran hukunci a gasar Seria A, biyo bayan rashin da’ar da ya nuna lokacin da Paulo Dybala ya maye gurbinsa yayin wasan da Juventus ta doke AC Milan da 2-1.

Talla

Ana mintuna na 55 ne Dybala ya maye gurbin Ronaldo, yayinda wasan yake matakin babu ci 0-0.

A lokacin da yake tattakin ficewa daga filin wasan ne Ronaldo ya fuskanci kocinsu Maurizio Sarri yana guna-guni, cikin fushi kuma yaki zama a benci ya ma fice daga harabar filin wasan gaba daya, kafin fafatawar tasu da AC Milan ta kare da kusan mintuna 5.

Wannan tasa a lokacin da yake tsokaci yayin zantawa da manema labarai kan lamarin, tsohon dan wasan kwallon kafar Italiya, Antonio Cassano ya ce, Ronaldo zai iya fuskantar haramcin buga wasanni har na tsawon shekaru 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI