Isa ga babban shafi
Wasanni

Saudiya za ta fara gasar kwallon kafa ta mata zalla

Wasu daga cikin matan Saudiya a filin wasa na Sarki Abdallah da ke birnin  Jeddah
Wasu daga cikin matan Saudiya a filin wasa na Sarki Abdallah da ke birnin Jeddah STRINGER / AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Spain Luis Rubiales ya bayyana cewa, za su taimaka wa Saudiya shirya gasar lig ta mata zalla, matakin da ke zuwa a daidai lokacin da Yarima Jiran Gado, Mohamed bin Salman ke bullo da sauye-sauye a kasar wadda a can baya aka sani da bin tsauraran dokokin Islama.

Talla

Rubiales ya bayyana haka a yayin da ake shirin gudanar da gasar Super Cup ta kwararrun kungiyoyin La Liga a birnin Jeddah na Saudiya nan da watan Janairu mai zuwa.

Kungiyoyin da za su fafata a wannan gasa sun hada da Barcelona da Real Madrid da Atletico Madrid da kuma Valencia.

Za a gudanar da wasannin ne a filin wasa na Sarki Abdallah mai daukar nauyin ‘yan kallo dubu 62 a birnin Jeddah.

Barcelona za ta kara da Atletico Madrid, yayin da Valencia ta fafata da Real Madrid kafin a gudanar da wasan karshe a ranar 12 ga watan na Janairu mai zuwa.

Yarima Mohamed bin Salman ya kawo sauye-sauye a Saudiya, inda ya dage dokar haramacin gudanar da wasannin kade-kade da raye-raye, yayin da kuma ya bude gidajen Sinima, baya ga bai wa mata damar fara tukin mota da kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.