Wasanni-Kwallon kafa

Bayern Munich na sha'awar dawo da Guardiola

Pep Guardiola
Pep Guardiola Reuters/John Sibley

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich na kokarin ganin ta dawo da tsohon kocin ta, Pep Guardiola don ya ci gaba da horar da’yan wasan ta a Alianz Arena a kaka mai zuwa.

Talla

Kungiyar ta kasar Jamus dake wasa a gasar Bundeligar kasar tana neman wandazai maye gurbin mai horar da ‘yan wasan ta Niko Kovac da ta sallama kwanan nan ne, kuma Guardiola na cikin kocawa 3 da take hangen daukowa.

Kocin Paris Saint Germain Thomas Tuchel da na Ajax Erik ten Hag an cikin wadanda take zawarcinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.