Wasanni-Kwallon kafa

David Villa zai yi murabus daga kwallon kafa

David Villa sanye da kayan Horo na kasar Spain.
David Villa sanye da kayan Horo na kasar Spain. REUTERS/Andrew Innerarity

Dan wasan da ya fi kowane dan wasa jefa kwallaye a raga a gasar Laligar Spain, David Villa zai yi murabus a watan gobe, a karshen kakar gasar J- League ta Japan.

Talla

Tsohon dan wasan Barcelona din zai rataya takalma bayan shekara 19 yana murza tamaula, inda a shekarar 2010 ya lashe kofin duniya da kasar Spain, bayan kofin nahiyar Turai da ya ci a shekarar 2008.

Dan shekara 37 din wanda ya ci kofunan Laliga 2 da Barcelona da kuma kofin zakarun nahiyar Turai, ya ce ya dade yana tunanin rataya takalma.

Villa wanda yake wasa a Vissel Kobe bayan ya kwashe shekaru 4 a Amurka da kungiyar New York City, zai kasance mai hannun jari a kungiyar Queensboro, kungiyar da ke bugawa a rukuni na biyu na gasar kwallon kafa a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI