Wasanni-Kwallon kafa

FIFA ta ba Wenger babban mukami

Arsenal Wenger took over at Arsenal in 1996 and revolutionised the approach to football in England.
Arsenal Wenger took over at Arsenal in 1996 and revolutionised the approach to football in England. Reuters/Scott Heppell

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA,a yau Laraba ta bayyana Arsene Wenger a matsayin jagoran bunkasa kwallon kafa na duniya.

Talla

FIFA ta ce tsohon kocin na Arsenal da Monaco zai kasance mai lura da bunkasa harkar tamaula ta maza da mata a duniya, kuma zai jagoranci ayyukan da suka shafi kwararru a wasan har ma da wadanda suka shafi sauye – sauye a wasan kwallon kafa.

Hukumar ta kara da cewa Wenger mai shekaru 70 zai kasance mai kula da abin da ya shafi horar da masu hora da kwallon kafa, sannan kuma ya tallafa a wani shirin shigar da tsaffin ‘yan wasa cikin harkar tafiyar da wasan.

Wenger wanda ya bayyana farin cikin sa a wata sanarwa, ya ce "na dade ina matukar dakon karbar wannan kalubale ".

Wannan sabon mukamin ya maido da Wenger harkar kwallon kafa a karon farko tun shekarar 2018 daya bar horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ya yi shekaru 22 yana horarwa.

Wenger ya sanya Arsenal cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai, inda ya lashe kofin Firimiyar Ingila 3, FA 7, ya kuma kai ta wasan karshe na gasar zakarun Turai a shekarar 2006.

A ranar Asabar Wenger ya musanta ikirarin da Bayern Munich ta yi cewa ta yi watsi da bukatar da ya mika mata na neman aikin horar da’yan wasanta bayan ta sallami Niko Kovac.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.