Wasanni

Osimhen ya sha alwashin goge tarihin da Yekini ya kafa

Victor Osimhen.
Victor Osimhen. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Matashin dan wasan Najeriya na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen mai shekaru 20, dake kungiyar Lille a Faransa, ya sha alwashin goge tarihin da marigayi Rashidi Yekini ya kafa na zama kan gaba wajen ci wa kasarsa kwallaye.

Talla

Osimhen ya sha alwashin ne kafin wasan da Najeriya ta lallasa Lesotho da kwallaye 4-2 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika.

Yayin wasan Osimhen ne ya ci 2 cikin kwallaye 4 da suka zura a ragar Lesotho.

Yanzu haka dai cikin wasanni 8 da ya bugawa Najeriya, Osimhen na da kwallaye 4, yayinda a gasar Ligue 1 dake Faransa, har yanzu shi ne dan wasa na 3 mafi daraja, a ajin matasa.

Har yanzu marigayi Rashidi Yakini ke rike da kambin adadin kwallaye mafi yawa da ya ci wa Najeriya, bayan da ya jefa 37 cikin wasanni 58 da ya fafata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.