Wasanni

Enrique ya sake karbar aikin horas da 'yan wasan Spain

Tsohon kocin kungiyar Barcelona, dake horas da 'yan wasan Spain Luis Enrique.
Tsohon kocin kungiyar Barcelona, dake horas da 'yan wasan Spain Luis Enrique. REUTERS

Hukumar kwallon kafar Spain ta ce, Luis Enrique ya sake karbar aikin horas da tawagar kwallon kafar kasar.

Talla

Enrique yayi wa tsohon aikin nasa kome ne, yayinda Spain ke tunkarar gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai da za a soma cikin watan Yunin shekarar 2020.

A watan Yunin da ya gabata Enrigque ya ajiya aikinsa domin kula da lafiyar ‘yarsa Xana, lokacin ne kuma mataimakinsa Robert Moreno, ya karbi jagoranci horas da ‘yan wasan na Spain.

A watan Agustan nan da ya gabata ne kuma diyar Luis Enrique din Xana ta rasu bayan fama da cutar Kansa.

Dama dai tun a shekarar 2018 da Spain ta dauke shi a matsayin koci, aka kayyade yarjejeniyar da suka kulla zuwa shekarar 2022, bayan kammala gasar cin kofin duniya da Qatar zata karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.