Wasanni-Kwallon kafa

Ku yi hakuri da Emery - Thierry Henry

Thierry Henry, tsohon dan wasan Arsenal
Thierry Henry, tsohon dan wasan Arsenal AFP/Valery HACHE

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake Ingila, Thierry Henry yana mai ra’ayin cewa kamata ya yi kungiyar ta mantadabatun lashe kofin gasar Firimya, ta kwallafa rai a kammalawa cikin kungiyoyi hudu na farko.

Talla

Henry ya kuma bukaci magoya bayan kungiyar da su baiwa kocin Unai Emery lokaci don ya kintsa kungiyar, ya dora ta kan seti.

Tun a kakar wasan 2015 da16 Arsenal ba ta samu tikitin shiga gasar zakarun nahiyarTurai ba, kuma mummunan kayen data sha a baya – bayan nan shine ci 10 – 2 jimilla a hannun Bayern Munich a gasar Zakarun Turai.

Maki daya ne ya hana ta zuwa gasar a bara, amma kuma Manchester City data lashe gasar FirimiyarIngila a kakar ta ba ta ratar maki 28.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI