Wasanni-Kwallon kafa

Zan kawo farin ciki da walwala Tottenham - Mourinho

José Mourinho.
José Mourinho. Reuters/Carl Recine/File Photo

Sabon mai horar da Tottenham, Jose Mourinho ya sha alwashin dagiya tare da kawo farin ciki da walwala a kungiyar, biyo bayan nadinsa a matsayin kocin kungiyar a ranar Laraba, sa’o’i bayan sallamar Mauricio Pochettino.

Talla

Mourinho ya bayyana matukar farin ciki da kasancewa sabon kocin Tottenham inda ya ce jajircewar magoya baya da ‘yan wasan kungiyar ce ta birge shi har ya karbi kalubalen.

Tun a watan Disamban bara dan shekara 56 ya rabu da aikin horar da ‘yan wasan tamaula sakamakon sallamar sa da kungiyar Manchester United ta yi da shi.

Tottenham ta kai wasan karshe a gasar zakarun nahiyar Turai a kakar wasan bara, amma a yanzu haka tana matsayi na 14 a kusan karshen teburin gasar Firimiyar Ingila, bayan nasarori uku kacal a wasanni 12.

Maki 11 ne ya raba su da matsayi na 4, inda daga nan ne ake samun gurbin fafatawa a gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.