Wasanni-Kwallon kafa

Aguero zai yi makonni yana jinya - Guardiola

Sergio Aguero dan wasan Manchester City
Sergio Aguero dan wasan Manchester City REUTERS/Andrew Yates

Mai horar da ‘yan wasan Manchester City, Pep Guardiola ya tabbatar da cewa shahararren dan wasan kungiyar, Sergio Aguero zai yi jinyar ‘yan makonni, sakamakon raunin da ya samu a kafarsa a wasan su na Asabar da Chelsea.

Talla

Dan wasan na Argentina Aguero, mai shekaru 31, ya fita daga fili da dingishi bayan minti na 77 a wasan da City ta samu galaba kan Chelsea da ci 2-1.

Guardiola ya kara da cewa aikin al’ajibi ne kawai zai iya dawowa da Aguero fagen tamola wani lokaci nan kusa, har ya iya fafata a wasan hamayya tsakanin kungiyarsa da Manchester United a ranar 7 ga watan Disamba.

Gabriel Jesus, wanda mafi akasarin wasannin da ya buga a wannan kaka daga benci ya faro su, shi ne zai maye gurbin Aguero har sai ya murmure.

Raunin Aguero dai shine na baya- bayan nan a City, saboda akwai ‘yan wasan kungiyar, Aymeric Laporte, da Leroy Sane da Oleksandr Zinchenko da ke jinya a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI