Wasanni-Kwallon kafa

Ku daina yi wa Bale ihu - Zidane

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale.
Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale. REUTERS/Javier Barbancho

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi kira ga magoya bayan kungiyar da su daina yi wa Gareth Bale ihu da tsangwama.

Talla

Dan wasan na kasar Wales bai samu tarba mai armashi ba lokacin daya shiga wasu a matsayin wanda ya canji wani, a karawar da Madrid ta Doke Real Sociedad da ci 3-1.

Wannan ne karon farko da Bale ya yi wasa cikin makonni 7 tun bayan da cece –kucen da daga tutar Wales da Golf da Madrid ya yi ya janyo yayin wasan da ya buga wa kasar sa a Cardiff.

Zidane ya ce ana yawan surutu a kan Bale, saboda haka shi yanzu so yake a sakam mai mara ya mayar da hankali saboda yana son ci gaba da zama a Madrid.

Dangantaka tsakanin Bale da magoya bayan Madrid a Santiago Bernabeu ba ta da armashi tun da ya koma kungiyar daga Tottenham a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 85 a matsayin dan wasa mafi tsada a lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI