Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Messi ne ya cancanci lashe kyautar Ballon d'Or a bana- Mbappe

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Kyllian Mbappe.
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Kyllian Mbappe. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Dan wasan gaba na PSG Kyllian Mbappe ya ce yana da yakinin Lionel Messi ne zai sake lashe kyautar Ballon d’Or a wannan karon ganin irin bajintar da ya nuna a kakar wasan da ta gabata.

Talla

Mbappe wanda har da shi kansa a jerin tarin ‘yan wasa 30 da za a tantance gwarzon a cikinsu, ya ce a iya tunaninsa babu dan wasan da ya nuna bajinta a fagen tamaula cikin kakar da ta gabata fiye da Messi.

Ko a watan Satumban da ya gabata ma dai, Messi ya doke tsohon abokin dabinsa Cristiano Ronaldo da kuma Virgil Van Dijk na Liverpool wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan shkara na FIFA ko da dai zaben ya zo da korafe korafe la’akari da yadda dadama daga masu kada kuri’a suka yi zargin zuraren kuri’u aka yiwa dan wasan.

A wannan karon ma dai yayin bikin bayar da kyautar a watan gobe, Messin zai kara da Ronaldo da kuma Van Dijk ne baya ga manyan zakakuran ‘yan wasa ciki har da Muhammad Salah na Masar da Sadio Mane na Senegal da Roberto Firmino na Brazil da Alexander Arnold dukkanninsu daga Liverpool baya ‘yan wasan Manchester City 4 da na Tottenham 2 sai kumja dan wasan Arsenal guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.