Wasanni-Kwallon kafa

Manyan Arsenal na baya na - Emery

Kocin Arsenal, Unai Emery
Kocin Arsenal, Unai Emery REUTERS/David Klein

Mai horar da ’yan wasan Arsenal, Unai Emery ya ce ba shakka yana da daurin gindin magabata a kungiyar, yayin da ake ta kiraye – kirayen a sallame shi.

Talla

A yau Alhamis Arsenal za ta karbi bakuncin Eintract Frankfurt a gasar Turai ta Europa, kuma za ta shiga wannan wasa ne bayan ta yi wasanni 6 ba tare da ta samu nasara ba a dukkan gasanni.

Canjaras din da Arsenal ta yi 2-2 da Southampton a ranar Asabar, ta janyo ihu da korafi daga magoya baya, inda wasu ma suka fito fili su na mai kira da a yi hannun riga da Emery.

Sai dai duk da wadannan kiraye – kiraye na sallamar dan shekara 48 din, shine dai zai jagoranci Arsenal a fafatawar da za ta yi da Frankfurt, kuma har yanzu yana tinkaho da tutiyar cewa kusoshi a kungiyar kamar su Raul Sanllehi, da daraktan kwararru Edu da ma sauran masu kunbar susa a kungiyar suna bayansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI