Wasanni-Kwallon kafa

Arsenal na neman sabon koci bayan sallamar Emery

Tsohon kocin Arsenal  Unai Emery.
Tsohon kocin Arsenal Unai Emery. © Action Images via Reuters/Paul Childs

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na neman sabon mai horarwa, biyo bayan sallamar Unai Emery wanda ya shafe watanni 18 yana jagorancin kungiyar.

Talla

Cikin wadanda ake sa ran za su maye gurbinsa akwai Nuno Espirito, wanda tsohon mai tsaron raga ne kuma ya birge a aikin horar da ‘yan wasan Wolves ta Ingila. Ya jagorance su zuwa gasar Firimiya daga karamar gasa, kuma daga nan suka ci ci gaba da zama, har suka samu shiga gasar Europa, har matakin sili daya kwale. Dan shekara 45 din ya fuskanci kalubalen rashin katabus a kungiyoyi biyu da ya horar a baya, Valencia da Porto.

Akwai Massimiliano Allegri, mai shekaru 52. Idan har mai yawan kofuna da lambobin yabo ne ake nema, to an samu a gun tsohon mai horar da Juventus din. Sau shida ya lashe gasar serie A ta Italiya, sannan sau biyu yana zuwa wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai. Sai dai ya ce rashin jin Ingilishi ne matsalarsa.

Akwai Freddie Ljungberg, wanda tsohon dan wasan Arsenal ne, kuma shi aka nada a matsayin kocin riko, amma matsalar ita ce bai taba horar da babbar tawagar kwallon kafa ba.

Sai kuma Mikel Arteta, wanda shi ma ya buga wasa a tawagar tsohon koci Arsene Wenger daga shekarar 2011 zuwa 2016. Yana aiki ne a matsayin mataimakin kocin Manchester City Pep Guardiola. Sai dai shi ma bai taba tafiyar da kungiya shi kadai ba.

Akwai kuma Eddie Howe, wanda ya ba mara da kunya a kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, inda ya karfafa ta, ya maida ta mai fada – a – ji. Sai dai yawancin kungiyoyi ba sa cika son daukan masu horarwa ‘yan asalin Ingila.

Baya ga wadannan daaka zayyano, akwai manyan kocawa daake ganin suna iya samun wannan aiki na horar da ‘yan wasan Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI