Wasanni-Tennis

Dan Najeriya Aruna Quadri ne zakaran Tennis na Afrika

Aruna Quadri dan Najeriya lamba 1 a fagen Tennis a Afrika.
Aruna Quadri dan Najeriya lamba 1 a fagen Tennis a Afrika. NAN

Sabon jadawalin hukumar kula da wasanni Tennis na duniya a bana ya sake tabbatar da Aruna Quadri dan Najeriya a matsayin lamba 1 a Afrika haka zalika na 20 a duniya.

Talla

Jadawalin na Disamba ya nuna cewa, Quadri ya dagaa daga koma bayan da ya fuskanta a watan Janairun shekarar nan inda ya kai na 26 a duniya, ko da dai ko a wancan lokaci matsayinsa bai sauya a nahiyar Afrika ba.

Ko cikin watan Satumban da ya gabata ma, Aruna Quadri sai da ya kai matsayin na 19 a duniya a fagen na Tennis ko da dai yanzu zai karkare wannan shekara a matsayinsa na 20 kuma zakaran Afrika, matsayin da ya jima yana rike da shi.

Sauran ‘yan wasan Tennis na Afrika da likkafarsu ta daga a jadawalin sun hadarda Omar Assar dan Masar da ya koma matsayin na 28 daga matakin 34 da yake a baya yayinda yak e matsayin na 2 a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.