Wasanni-Kwallon kafa

Lokacin ritaya na kara kusantowa gareni- Messi

Zakaran kwallon kafa na duniya a bana Lionel Messi wanda a wannan karon yayi nasarar lashe kyautar Ballon d’Or karo na 6, ya amsa cewa tabbas ritaya daga fagen tamaula na sake kusantowa gareshi.

Lionel Messi.
Lionel Messi. Christian Hartmann/Reuters
Talla

A wata zantawarsa da mujallar wasanni can a Spain, Messi mai shekaru 32 ya bayyana cewa Barcelona na da cikakkiyar masaniya kan sauya shekarsa ko kuma rataye takalmi dungurugum la’akari dacewa kwantiragin da ya ke ka a yanzu ya sahale masa rabuwa da Club din a kowanne lokaci.

Har yanzu dai za a iya cewa dan wasan ya bar tarin magoya bayansa a duhu don kuwa bai fayyace Club din da ya ke shirin komawa ba, ko da dai akwai jita-jitar da ke nuna cewa ya samu goron gayyata daga David Becham don komawa Amurka da taka leda.

Yanzu haka dai Messi ya yiwa takwaransa kuma tsohon abokin dabinsa Cristiano Ronaldo na Juventus fintinkau bayanda tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa yayinda za a iya cewa Ronaldon kuma tauraruwarsa ke neman disashewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI