Wasanni-Kwallon kafa

Neymar da Mbappe sun ci wa PSG kwallaye a daren Laraba

Neymar da Mbappé yayin wani wasa
Neymar da Mbappé yayin wani wasa FRANCK FIFE / AFP

Neymar da Kylian Mbappe sun ci wa Paris Saint Germain kwallo daya kowanne a wasan da suka samu nasara 2-0 kan Nantes a daren Laraba.

Talla

Mbappe ne ya fara saka kwallo bayan dawowa daga hutu, yayin da kusan karshen wasa Neymar ya ci tasa kwallon daga bugun daga kai – sai – mai – tsaron – raga kusan karshen wasan da ya gudana a filin wasa na Parc des Princes.

Wannan nasarar ta sa yanzu PSG na kan gaba a teburin gasar Ligue 1 da tazarar maki biyar.

PSG wacce a karshen makon da ya gabata ya kamata ta fafata da Monaco amma aka dage wasan saboda rashin kyaun yanayi, tana da wani kwanten wasa da za ta gwabza da Marselle, a kokarin da ta ke na lashe kofin Ligue 1 na 7 a kakan wasanni 8.

Kocin PSG Thomas Tuchel ya fara wasan da Neymar da Mbappe a lokaci guda a karon farko cikin wannan kaka, yayin da ya bar Edinson Cavani da Mauro Icardi a benchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI