Wasanni-Kwallon kafa

Soslkjaer ya jinjina wa Rashford kan wasan United da Tottenham

Kocin Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer yana magana da Marcus Rashford yayin wani wasa.
Kocin Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer yana magana da Marcus Rashford yayin wani wasa. REUTERS/Andrew Yates

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya jinjina wa dan wasan gaban kungiyar, Marcus Rashford dangane da irin rawar da ya taka a wasan da kunigiyar ta gwabza da Tottenham a jiya Laraba.

Talla

Rashford yaci kwallaye 2 a wasan da aka tashi 2-1, abin da ke nufin cewa yana da kwallaye 9 a wasanni 10 da ya buga a baya- bayan nan, sai dai abin da ya fi ma jan hankalin Solskjaer shine yadda Rashford ya murza tamola a karawar.

Dan shekara 22 din ya kasance wa ‘yan wasan bayan Tottenham tamkar annoba a wasan tun daga farawa a karkarewa, inda har sai da ya samu bugun daga –kai – sai – mai- tsaron – raga sakamakon rafke shi da suka yi saboda tsananin takaici.

Sakamkon wannan wasa dai ya mayar da Manchester United cikin manyan kungiyoyi shida da ke kan gaba a gasar Firimiyar Ingila karon farko tun a watan Satumba.

Tsohon kocin Manchester United, Jose Mourinho dai shine yake horar da Tottenham a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.